Tawagogin makoki na ƙungiyoyin addini, a ranar tunawa da rasuwar Annabi Mai Girma (SAW) da shahadar Imam Hasan Mujtaba (AS), sun halarci harami mai tsarki na Sayydah Fatimah Ma’asumah (AS) inda suka gudanar da makoki da zaman jaje.
A ranar tunawa da shahadar Imam Al-Ridha (AS), an gudanar da taron makoki da zaman juyayi tare da halartar Ayatullah Makarim Shirazi, inda suka yi makoki da zaman juyayi don shahadar Imam na takwas na mabiya Ahlal Bait As.
A yau Alhamis (13ga Agusta 2026) daidai da ranar 29 Safar 1448, ranar tunawa da shahadar Imam Ali Ibn Musa Ridha (AS), masu hidima na haramin Sayyidah Fatmah Ma’asumah Karimatu Ahlul-Bayt (AS) sun yi tattaki daga Masallacin Imam Hasan Al-Askari (AS) don mika ta'aziyya ga 'yar'uwar Imam Al-Ridha (AS) zuwa haramin Sayyidah Fatimah Ma’asuma (AS).