Kafofin yada labarai na duniyar Larabawa tun daga Yemen da Lebanon zuwa Iraki da Qatar, sun gudanar da cikakken rahoto kaitsaye na taron bankwana da jana'izar shahidin jagoran juyin juya hali, tare da bayyana wannan taro a matsayin "Jana'izar Ƙarni," sun haskaka halartar miliyoyin mutane, sakonnin tsayin daka da kasancewar kwamitocin kasashen waje daga kusan kasashe 100, kuma sun ɗauki shi a matsayin alamar ci gaba da hanyar juyin juya halin Musulunci da kuma jigon gwagwarmaya.