Manzan Allah ( s.a.w.a) ya rayu shekaru 63 a duniya yana mai isar da sakon addinin Musulunci, ya canza alqibalar halinta daga bautar gumaka da sauransu zuwa bautar Allah Ta’ala shi kadai, sannan a hajin da Manzan Allah yayi wacce itace guda daya da yayi a duniya, kuma a wannan hajin ya koyama al’ummarsa abubuwa da dama da kuma hukunce-hukunce wadanda suka doru akan al’ummarsa, ya kuma isar da sako na karshe a cikin wannan addini na musulnci, ya kuma bayyana sokon wanda da isar da wannan sakon ne musulunci ya cika ta hanyar bayyanawa al,ummarsa wadanda za su ci gaba da jagorantar wannan addini da kuma bayyana shi, kamar yadda yazo a hadisin da Imam Muslim ya fitar a sahihinsa cewa: Manzan Allah ( s,a, w,w) yace: Kalifofi a bayana su goma sha biyu ne dukkanin su quraishawane....