Abdul Bari Atwan, babban manazarcin harkokin dabaru na yankin, a cikin wata makala, yana mai nuni ga sabuwar dabarar Donald Trump na killacewa da takunkumin tattalin arziki a kan Iran, ya rubuta cewa, komawa ga wannan dabara yana nufin rashin nasarar zaɓin soji wajen cimma burin wannan yaƙi, kuma ya jaddada cewa, takunkumin tattalin arziki, kamar zaɓin soji ne, shi ma zai sha kaye, domin Iran ƙasa ce mai girma kamar nahiya, tana da yawan jama'a sama da miliyan 95, kuma ƙasarta mai albarka ce, ba za ta taɓa jin yunwa ba.