Ayatullah Sayyid Mujtaba Hussaini Khamene'i ya fitar da saƙo inda ya yi godiya ta musamman ga halartar dubban miliyoyin al'ummar Iran da Iraki a jana'izar "Shahidin Iran", sannan ya ce wa Shahidin al'umma: "Mun yi alkawari cewa za mu ɗauki fansar jininka mai tsarki da jinin dukkan shahidan waɗannan yaƙe-yaƙe biyu a kan masu aikata wannan mummunan laifi marasa daraja. Wannan fansa ita ce buƙatar al'ummarmu, kuma babu shakka dole ne ta tabbata. Wadannan masu laifi, waɗanda aka san su tun daga manyansu har zuwa ƙananansu, za su tafi kabari tare da burin mutuwa cikin kwanciyar hankali wanda ba zai taɓa cika ba."
Tehran a yau ba wai kawai ta yi jana'izar jagoranta ba ne; Tehran a yau ta canja daga makoki zuwa yunkuri, daga zaman makoki zuwa ramuwa. Miliyoyin mutane, kai mu ce, miliyoyin tsaunuka masu aman wuta da suke tafarfasa waɗanda suke bubbugowa da zurfafan zukatansu suna masu shelenta neman fansar jini, sun mayar da titunan babban birnin zuwa tekun jajayen tutoci. Jajayen tutocin da ba iya alamar makoki su ke ba, har ma alamar guguwa ce da ke kan hanyar bayyana. Guguwa irin ta Mukhtar. Guguwa irin ta yunkuri. Guguwar da ta yi alkawarin kawar da girman kai na duniya. A yau Iran ba wai kawai ta raka jagora ba ne; a yau Iran, da jinin wanda ake zalunta, ta yi mubaya'a ga yaƙin maras aminci.