4 Disamba 2019 - 04:16
​Iran Ta Yi Watsi Da Rahoton Amnesty Kan Mutuwar Masu Zanga zanga

Mahukunatn Tehran, sun yi watsi da rahoton kungiyar kare hakkin bil adama ta kasa da kasa Amesty International, mai cewa mutane akalla 208 ne suka rasa rayukansu a zanga zangar da wasu ‘yan kasar sukayi kwanan baya kan karion farashin maid a gwamnatin kasar ta yi.

(ABNA24.com) Mahukunatn Tehran, sun yi watsi da rahoton kungiyar kare hakkin bil adama ta kasa da kasa Amesty International, mai cewa mutane akalla 208 ne suka rasa rayukansu a zanga zangar da wasu ‘yan kasar sukayi kwanan baya kan karion farashin maid a gwamnatin kasar ta yi.

Da ya ke bayyana hakan a gidan talabijin din kasar, kakakin ma’aikatar shari’a ta kasar, Gholam-hossein Esmaili, ya yi, ya ce babu kanshin gaski ko kadan ga wadanan alkalumman na makiyan kasar.

Mista Esmaili, ya ce rahoton na karya ya kunshi wasu sunaye, na wasu mutane dake raya yanzu haka da kuma wasu da sukayi mutune da suka rasu.

A rahoton baya baya nan data fitar kungiyar ta Amnesty, dake da mazauni a birnin Landan, ta ce mutane 208 ne suka mutu a zanga zangar ta kin jinin Karin farashin mai a Iran, a tsakiyar watan Nuwamba da ya gabata, bayan tun farko ta sanar da adadin mutane 161, batun da mahukuntan na Iran ke ci gaba da musantawa.



/129