Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : tsk
Litinin

16 Yuli 2018

16:18:20
901939

GWARA DAN SHI'A SAU DUBU DA DAN IZALA  ---- Inji Sheikh Abduljabbar Nasir Kabara..

A Karatun littafin Muqaddimatul Azeefa na ranar Juma'a, 29/6/2018, wanda Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara ya gabatar a Masallacin Jami'u Amiril Jaishi dake birnin Kano ya bayyana cewa gwara dan shi'a sau dubu da dan izala kuma yace a ilmance ya fadi wannan maganar.  Shehin Malamin yace:

.. Mu daina tsoron su ce mana- ai dai kun ji gashi, har Annabi sun ce masa Rafidhy, Sayyidina Ali Rafidhy, AlHassan da AlHusaini da zuriyyarsu tsarkaka Rafidha, wato Shuyukhur Rafidha. Mun karanta ko? Kuma mun karanta daku kun ji kalmar Attashayyu' shianci makami ne amma na kugere irin wanda mazawayin kasuwa yake rikewa yana bawa yara tsoro amma hakika ba makami bane. Wata kalma ce- Na'am, akwai shianci bama musawa, akwai ma'akhizu a cikin shianci bama musawa, saidai kalmar shiancin ana amfani da ita a wasu lamurra wanda bama magana shiancin bane kwata kwata.

 " Ah, mu yanzu mu 'yan shia ne a wajensu? Dukkansu sun sani, ai sun sani. Allah ne ya rufa masu asiri da na gane nayi shia da sun banu. To wa zan ji tsoro in shia nake? Dan izala ma ya iya cewa izala ne. Wannan na sha fada, na sha fada, abu daya ne yasa ni ba zan amsa sunan shia saboda ban yarda nayi intisabi ga sunan amma ba tsoron wani abu ba ko gudun wani abu ba, gamsuwa iyaka! Amma gwamma dan shia sau dubu da dan izala, wannan a ilmance nake fada, wanda ba haka ba mu zauna dashi.

 " In kace zagin Sahabbai sai ince wa ya kai yan izala zaginsu? Ah! Iya zagin da Ibn Taimiyyah yake ta yiwa Sayyidina Ali bai isa ba? Me ya raba shi dasu? Kuma in su sun zagi Sayyidina Abubakar, shi ba Ali ya zaga ba? A ciki waye gaba? Domin ya inganta a littafanmu- a namu ba a na shia ba- Annabi yace duk wanda ya zagi Ali Ni Muhammadur Rasulullahi ya zaga amma inda yace wanda ya zagi Abubakar ni ya zaga. In akwai inda yace duk wanda ya zagi Abubakar Ni zaga a kawo min, babu. Kai da kake zagin wanda Annabi yace zaginsa ni aka zaga. Kai kake aibata kake zagin wanda zaginshi zagin Annabi ne. Na'am, zaginsa shima mummunan abu ne amma ba shi Annabi aka zaga ba. Ba wani nassi, Saidai ya zama mummuna ne aikin a matsayin girman wanda aka zaga, amma ba yanda zaka daidaita zagin Sayyidina Abubakar da zagin shugaban halitta. Amma zagin Sayyidina Ali Annabi ya daidaita shi da zagin shugaban halitta. Kun ga ko daga nan, a tsaya iya matsalar zagi zagi. To, su izala suna zagin wanda yafi wanda su shia suke zagi. Kenan, wanne yafi sharri cikinsu? Izala. Shia babba rigimarsu da Alu Abi Sufyan. Alu Abi Sufyan itace babbar rigimarsu. Amma izala fa? Da Alu Muhammadin suke, ko sunan basa son ji.... "