Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{A.S}-aba-Ayatullahi Wahid Khurasani, Ayatullahi Safi Ghulphaigani biyu daga cikin manyan maraja’a na shi’a ne suka fito yin tattaki da kuma juyayin shahadar Fadima{s.a} a garin Kum a yau talata. shi dai tattakin ya soma ne daga gidaje maraja’an zuwa Haramin Ma’asumma inda masu juyayin shahadar suka taru domin nuna bakin cikin su da abunda a kai ma iyalin Manzon Allah{s.a.w.w}.ABNA

24 Maris 2015 - 16:55