Taron zana'idar kwamanda shahid Haj Muhammad Ali Allah Dadi.

21 Janairu 2015 - 11:33

Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlulbaiti{A.S}-abna-da safiyar yau ne aka gabatar da zana'idar daya daga cikin kwamandoji kare juyin musulunci na Iran Shahid Haj Muhammad Ali Allah Dadi, anyi zana'idar ne a gaban ofishin dakarun kare juyin musulunci dake Tehran.

Kwamanda Ali  Allah Dadi ya samu Shahada ne tare da wasu dakarun Hizbullah sanadiyar harin da wani jirgin yaki mallakar Haramtarciyar Kasar Isra'ila ya kai masu a yankin kanitare Syria.

Bayan anyi masa Sallah a Tehran za a aika gawar a garinsu na haihuwa wato kirma idan za'a rufe shi.ABNA