A farkon wannan ziyarar, Manajan Daraktan Kamfanin Dillancin Labarai na ABNA, Hasan Sadrai Arif, ya gabatar da rahoton ayyukan ma’aikatu daban-daban na Kamfanin.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na cewa, Ayatullah Mohsen Faqihi mamba na kungiyar malamai ta Qum, ya halarci ofishin edita na kamfanin dillancin labarai na kasa da kasa ABNA a birnin Qum da yammacin jiya Laraba 09 ga watan Afrilu 2025, domin yi masa bayani kan ayyukan Kamfanin. Bayan kammala wannan ziyara, Ayatullah Faqihi ya bayyana tare da manema labarai daga kamfanin dillancin labarai na ABNA, kuma a jawabin da ya gabatar ya bayyana manufofin kafafen yada labarai a halin da ake ciki da kuma muhimmancin kyawawan halayya a aikin jarida.
Your Comment