Sojojin kasar Iran sun kaddamar da sabbin ci gaban da suka samu na kayakin yaki wadanda suka kera a cikin gida.

26 Afirilu 2021 - 13:00

ABNA24 : Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa sojojin sun samar da sabbin kayakin yaki wadanda suka kera a cikin gida, wadanda kuma suka hada da sabon tsarin garkuwar sararin samania, jiragen wadanda ake sarrafasu daga nesa, da wasu kayakin lartarki wadanda ake amfani da su don harkokin tsaron kasa.

A yau lahadi ne aka baje kolin sabbin kayakin yakin wadanda sojojin suka samar, a wani baki na musamman da aka gudanar, tare da halattar mataimakin babban kwamadan sojojin kasar Rear admiral Habibollah Sayyari da kuma babban hafsan sojojin kasa na kasar Iran Burgedia Janar Kioumars Heydari.

Daga cikin kayakin da aka baje kolinsu akwai na’urar rada mai gano makiya da kuma wargaza kokarinsu na kutsawa cikin tsarin tsaron kasar, da jiragen yaki, da jiragen wadanda ake sarrafa su daga nesa.

342/