An Fara Gudanar Da Jerin Gwanon Babrura Na Tunawa Da Ranar Cin Nasarar Juyin Musulunci A Iran
11 Faburairu 2021 - 13:02
Lambar labari: 1114314
ABNA24 : Da safiyar yau Laraba ne mahaya babura da motoci su ka yi jerin gwano domin munar zagayowar ranar da juyin musulunci a Iran ya kai ga cin nasara shekaru 42 da su ka wuce.
Ana yin jerin gwanon nan a ciki birane da garuruwa daban-daban na Iran cikin kula da matakan hana yaduwar cutar corona.
A shekarar 1979 ne yunkurin juyin musulunci a karkashin jagorancin marigayi Imam Khumain ya kai ga samun nasarar kifar da gwamnatin tsarin sarauta da shekaru 2500.
A tsawon daron jiya al’ummar Iran din sun rika bayar da kabarbari a saman gidajensu wanda yake tunawa da yadda ta kasance a ranar karshe ta mulkin tsarin sarauta.
342/