15 Oktoba 2019 - 04:32
​Dubban Yan Tunisia Suna Murna Da Zaben Kais Said A Matsayin Shugaban Kasa

Dubban mutanen kasar Tunisia sun fito kan tituna suna daga tutar kasar don nuna farin cikinsu da zaben Kais Sa’ied a matsayin shugaban kasa a zaben da aka gudanar a jiya Lahadi.

(ABNA24.com) Dubban mutanen kasar Tunisia sun fito kan tituna suna daga tutar kasar don nuna farin cikinsu da zaben Kais Sa’ied a matsayin shugaban kasa a zaben da aka gudanar a jiya Lahadi.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa mutanen kasar a birnin Tunis babban birnin kasar sun rufe wani babban titi a birnin mai suna Titin Habib Bogiba suna ta nuna farin cikinsu da sakamakon zaben wucin gadi wanda ya nuna cewa Kais Sa’id yana kan gaba da kimanin kashi 77%.na kuri’un da aka kada a zabe.

Kais Saed dai dan takarar shugaban kasa ne a zaben na jiya, amma wanda bai da jam’iyya, kuma shi ne a gaba a zaben zagaye na farko wanda aka gudanar a cikin watan da ya gabata, sannan a zagaye na biyu wanda aka gudanar a jiya Lahadi 13 ga watan Octoba, yana kan gaba, duk fa cewa kwamitin zaben kasar bata bayyana cikekken sakamakon zaben gaba daya ba.


/129