Tashar talabijin ta Almayadeen ta bayar da rahoton cewa, a yayin ganawar da ta gudana tsakanin Martin Griffiths da kuma Abdulmalik Al-huthi a jiya, bangarorin biyu sun tattauna kan batun yarjejeniyar dakatar da bude wuta da aka cimmawa a Sweden a kwanakin baya, inda manzon musamman na majalisar dinkin duniya ya yabawa Alhuthi dangane da yadda suke bayar da hadin kai ga gwamnatin tseratar da kasa a Sanaa wajen yin aiki da wannan yarjejeniya a Hudaidah da sauran wuraren da yarjejeniyar ta kunsa.
Kafin wannan lokacin dai a ranar Asabar Manzon musamman na majalisar dinkin duniya Martins Griffiths ya gana da shugaban majaliar koli ta juyin juya halia a kasar ta Yemen Muhammad Ali, da kuam ministan harkokin wajen kasar ta Yemen Hisham Sahraf, inda anan ma suka tattauna batun aiki da yarjejeniyar.
Masu sanya ido dai sun ce tun bayan cimma yarjejeniyar dakatar da bude wuta musammana garin Hudaidah a ranar 18 ga watan Disamban da ya gabata a birnin Stockholm na Sweden, Saudiyya ta kaddamar da hare-hare da jiragen yakia kan birnin na Hudaidah sau fiye da dari biyu.