Kotun, wacce ta yanke wannan hukuncin ranar Talata, ta kara da cewa ta dauki matakin ne saboda, acewarta, tunda sau daya ya sha rantsuwar kama aiki, to yana da damar tsayawa takara a zaben shugabancin kasar wanda za a yi ranar 28 ga wata Maris.
Kotun ta ce rantsuwar kama aikin da Mr Jonathan ya yi a shekarar 2010, ya yi ne domin ya kammala wa'adin mulkin shugaba Umaru Musa Yar'Adua, wanda ya rasu a shekarar.
Da ma dai wani dan kasar, Cyriacus Njoku ne ya kai karar Mr Jonathan a gaban kotun, yana mai kalubalantar cancantarsa ta yin takara a zaben 2015.
Sai dai alkalin kotun, Mai shari'a Abubakat Yahaya, ya ce wa'adi daya kawai Mr Jonathan ya yi, domin haka kundin tsarin mulkin kasar ya ba shi damar sake yin takara. ABNA