Taskar labaru ta ahlulbai abna ta rawaito- Ayatullahi sayyid hashim hussani bushahari shugaban hauzojin ilimi na kasa a rana ta biyu da fara taron maluman duniya akan hadarin masu kafirta musulmi wanda yake gudana a qom iran yace; baban bala’in da musulmi ke fuskanta a duniya shine matsalar masu wuce gona da iri wato masu kafrta musulmi.
Ya kara da cewa; kafirta musulmi wata fitinace da take kawo cikashin zaman lafiya tsakanin musulmi. Babu wata musiba wadda ta wuce masu kafirta musulmi [ takfiri] domin sun bata fuskar musulunci sun kuma sa mutane na kara nisa da addini gaskiya.
Hussaini bashahari yace; manzon Allah [s] shaikara 23 yayi yana kokarin isar da sako zuwa ga mutane .kura’ani ya bayyana musulunci da cewa addinin zaman lafiya ne. abunda muka fahimta da musulunci shine idan aka bamu ummarni yin jahadi to kuma an nunamana yadda akayin jahadin .duk wanda ya furta Kalmar shahada a mahangar maluman musulunci shi musulmine dukiyarsa da ransa ya haramta.
Shugaban hauzoji na kasa yace;abunda ya kawo akidara musu kafirta musulmi shine jahilci ,taasubanci, rashin fahimta kur’ani, yadda ya dace, yadda da jita-jita akan sauran mazahabobi suna daya daga cikin abunda ya haifar da wannan mummunar akidar. Wannan akidar suna fitar da duk wani wanda basu ba daga musulunci. Kuma suna ma makiya musulunci aiki duk da hare-haren da isra’il ke kaiwa akan falastinawa, amma yan takfir suna can suna kasha musulmi.
Ayatllahi hussaini yace; sakamakon wannan akidar mumuna yasa musulunci ya zama abun kyama a duniya kuma yana kawo ma musulmi fuskantar barazana a kasashe daban-daban.kuma sun kawo rabe-rabe tsakanin kasashen musulmi, wannan ya bude kofar shigowar kasashen yamma acikin kasashen musulmi , ta haka yasa musulmi sun mata da makiyan sun a asali.
Shugaban hauza yace; idan maluma basu hada kai da kuma samo hanyar rusa wannan akidar ba, to bada jimawaba zasu ga abunda zai faru domin wannan akidar zata mamaye wurare da dama. Dolen malumane su nunama matasa addini da kuma koyarwarsa kuma su fitar da fatawa ta hana kafirta musulmi musamman maluman ahlisunna.
Muna fatar zaman lafiya ya yadu akasashen musulmi. ABNA