30 Yuni 2014 - 12:06
An Sako jami'an Diflomasiyyan Tunisiya Biyu Da Aka Sace A Libya

An Sako jami'an Diflomasiyyan Tunisiya Biyu Da Aka Sace A Libya

Hukumomin kasar Tunisia sun tabbatarda sakin wasu jami’an diflomasiyan kasar biyu  da aka sace yau sama da watanni uku a birnin Tripoli na kasar Libiya. Jami’an diflomatisan biyu sun hada da Mohamed Ben Cheikh wanda aka sace ran 21 ga watan Maris da Al-Aroussi Kontassi wanda shi kwa akayi garkuwa dashi tun ran 17 ga watan April na wanan shekara. Majiyoyi daga kasar sun ce tuni wani jirgin saman soja ya isa da jami’an biyu a Tunus babban birnin kasar, inda aka shirya wa jami’an biyu tarbe a hukumance, wanda ya samu halartar shugaban kasar Moncef Marzouki, da fira- minista Mehdi Jomaa et da shugaban majalisar dokokin kasar Mustapha Ben Jaafar. Da yake bayani ga manema labarai, daya daga cikin jami’an da aka saki yace suna cikin lafiya kuma babu wata muzguna da suka fuskanta daga hannun wadanda suka yi garkuwa dasu tsaawan wani locacin.