Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: A Stockholm, jama'a masu yawa sun taru a dandalin Odensplan domin amsa kiran wasu kungiyoyin farar hula, suna neman a kawo karshen laifukan ta'addanci yaki na Isra'ila a Gaza.
A Athens, babban birnin Girka, masu zanga-zangar sun yi macci da tattaki zuwa ga ofisoshin jakadancin Isra'ila da Amurka.
A Paris, masu zanga-zangar kuma sun fito kan tituna don nuna goyon baya ga Falasdinawa.
A London, 'yan sanda sun fara wani babban aikin tsaro, kuma an gudanar da zanga-zanga da yawa a duk faɗin birnin.
.....................
Your Comment