17 Mayu 2026 - 02:09
Source: ABNA24
Manyan Bama-Bamai Sun Fashe A Beit Shemesh Isra'ila + Bidiyo

Ba jimawa an ji ƙara da turnikewar hayaki bayan mummunar fashewa abubuwa a Beit Shemesh da ke tsakiyar Falasdinu da aka mamaye. Garin Beit Shemesh da ke yammacin Kudus (Baitul Makdis), inda wata fashewa mai ban mamaki ta faru, wuri ne da ake ajiye manyan bama-bamai na nukiliyar Isra'ila.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Kafin wannan, wasu masu fafutukar kafofin yada labarai sun ce ana kyautata zaton an boye rukunin manyan bama-baman nukiliya a sansanin sojin sama na "Sdot Micha" da ke cikin garin Beit Shemesh ne wanda suka fashe daga baya.

Gidan talabijin na "Kan" na Isra'ila ya yi iƙirarin cewa: Fashewar da ta faru a yankin "Beit Shemesh", ta faru ne a cikin kamfanin "Tomer"; kamfanin da ke aiki a fannin haɓakawa da kera makamai masu linzami na tsaro da kai hari na Isra'ila.

Bayan faruwar lamarin Sojojin sahayoniya sun hana shigar da motocin agajin gaggawa da jami'an kashe gobara zuwa yankin da fashewar ta faru, hakan ya kara yawan cece-kuce game da ainihin yanayin fashewar Beit Shemesh.

Muhimmancin Yankin Da Fashewar Ta Taru A Falasdinu Da Aka Mamaye

Garin Beit Shemesh da ke yammacin Kudus, inda wani fashewa mai ban mamaki ya faru, wuri ne da ake ajiye manyan bama-bamai na nukiliyar Isra'ila.

Jami'an karamar hukumar Beit Shemesh sun yi iƙirarin cewa sun tayar da wasu bama-bamai da suka rage daga yaƙin da akayi, kuma babu wani abin damuwa. 

Amma Kafofin yada labarai na sahayoniyar sun ce: Fashewar a Beit Shemesh ba fashewa ce da aka tsara aka ahirya ba ce domin ba a sanar da ma'aikatan agajin gaggawa da jami'ai game da wani gwaji ko fashewa da aka shirya ba sun ƙara da cewa; to me ake boyewa? Da ba a ko gargadi mazauna yankunan da ke kusa ba kafin fashewar ba!!

Kafofin yada labarai na yahudawa a baya ga faruwar hakan sun ba da rahoton mummunar fashewa a yankin Beit Shemesh a yammacin Kudus da aka mamaye.

.......................

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha