17 Mayu 2026 - 00:18
Source: ABNA24
Hizbullah Na Ci Gaba Da Kai Hare-Haren Kan Sojojin Mamaya

Hizbullah ta Lebanon, a cikin bayanai da ta fitar, ta yi cikakken bayani game da hare-haren da ta kai kan wuraren sojojin gwamnatin Sahayoniya da kayan aikinsu na soja.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (AS) – ABNA - ya habarta cewa: Kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na Mehr ya ruwaito daga gidan talabijin na Al-Mayadeen, Ƙungiyar Jihadin Musulunci ta Lebanon ta sanar a cikin wata sanarwa cewa ta lalata wata babbar mota (bulldozer) mallakin sojojin mamaya da ke gaba daga shiga garin Rashaf zuwa wajen garin Hadatha, ta hanyar fashewar bama-bamai.

Ƙungiyar ta kara da cewa bayan wannan harin, wasu runduna ta motocin yaki na abokan gaba sun shiga wurin domin ba da taimako da kuma dauke motar da aka lalata, amma sun fada ciki harin nakiyoyin Hizbullah tare da lalata su ma.

Hizbullah ta kara da cewa abokan gaba daga baya sun kwashe wadanda suka suka mutu da raunata a karkashin bude wuta mai tsanani da hayaki mai yawa.

Haka kuma, rahotanni sun ce Hizbullah ta kai hari da makamai masu linzami da dama a kan wuraren mamaya a garin al-Bayyadah, kuma ta kai hari kan taron sojojin mamaya a al-Bayyadah da Deir Siryan da hari mai tsanani.

Wadannan hare-haren suna zuwa ne biyo bayan keta yarjejeniyar tsagaita wuta daga bangaren gwamnatin Sahayoniya ta hanyar kai hari a wasu yankuna na kudancin Lebanon.

Jiya an sanar da cewa gwamnatin Sahayoniya da Lebanon sun amince da tsawaita tsagaita wuta na kwanaki 45, tsagaita wutar da a zahiri ba a aiwatar da ita ba, kuma gwamnatin Sahayoniya na ci gaba da hare-haren ta a kudancin Lebanon.

Sakamakon wadannan hare-haren, ya zuwa yanzu mutane da dama sun yi shahada wasu sun jikkata.

Dangane da haka, Ma'aikatar Lafiya ta Lebanon ta bayyana cewa adadin shahidai hare-haren gwamnatin Sahayoniya a Lebanon tun daga ranar 2 ga Maris, 2026 ya kai 2,969.

Your Comment

You are replying to: .
captcha