Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarto bisa nakaltowa daga Kamfanin Dillancin Labaran Hauza cewa: Sheikh Zakzaky wanda a duk shekara ya kan gana da mabiyansa bayan kammala watan Ramadan, ya fara jawabin nasa da taya murnar sallah. Ya kuma yi ishara da yanayin da watan Ramadan na wannan shekara ya zo da shi, inda ya ce: “Ko da yake wannan shekarar ta zo da wasu ƙalubale, amma muna gode wa Allah da ya sa mun ga farkon azumi da ƙarshensa lafiya.”
Hare-Haren Baya-Bayan Nan Kan Iran
Da yake bayani kan hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kai wa Iran, ya ce: “Tun daga watan Rajab makiya suka fara tara makamai a kewayen Iran domin shiryawa kai hari. Hare-haren farko sun shafi gidan Sayyid Qa’id da kuma wasu makarantu na ‘yan mata da na maza, inda aka kashe dalibai da fararen hula da dama.”
Ya kuma kara da cewa wasu daga cikin wadannan hare-hare an kai su ne daga Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) da Bahrain, yana mai cewa: “Harin da aka kai wa gidan Sayyid Qa'id daga UAE aka harba shi, sannan harin da aka kai kan dalibai daga Bahrain ne. Duk da cewa akwai yarjejeniya tsakanin wadannan kasashe da Iran cewa ba za a yi amfani da kasashensu wajen kai hari kan Iran ba.”
Hari Kan Tattalin Arzikin Iran
Jagoran Harkar Musulunci ya bayyana cewa daga baya makiya sun fara kai hari kan abubuwan more rayuwar tattalin arziki na Iran, yana mai cewa: “Sun kai hari kan masana’antar karfe, masana’antar siminti da kuma cibiyoyin samar da wutar lantarki domin durkusar da tattalin arzikin Iran. A gefe guda kuma Iran ta mayar da martani kan cibiyoyin makiya da ke cikin wasu kasashen Larabawa.”
Ya jaddada cewa: “Iran ba ta taba kai hari kan fararen hula ba, martanin da take mayarwa yana kan sansanonin sojin Amurka ne kawai, domin Amurka ta yi amfani da kasashen nan wajen kai hari kan Iran.”
Babban Dalilin Yakin
A cewar Sheikh Zakzaky, tsawon sama da shekaru 40 Isra’ila na jiran shugaban Amurka da zai kai wa Iran hari. “Trump ya aikata hakan ne bayan Isra’ila ta zuga shi. Sun yi zaton idan Amurka ta kai hari, Iran za ta rushe. Saboda haka babban dalilin wannan gaba shi ne rawar da Iran ke takawa wajen hana kafa “Babbar Isra’ila.”
Sansanonin Amurka A Kasashen Larabawa
Da yake magana kan kasancewar sojojin Amurka a yankin Gulf, ya ce: “Ba a kafa wadannan sansanoni don kare kasashen Larabawa ba, an kafa su ne domin kare shirin samar da Babbar Isra’ila ne”
Rawar Iran Wajen Taimakon Falasdinu
Sheikh Zakzaky ya kuma jaddada cewa Iran tana taimakon Falasdinu ne saboda alhakin addinin Musulunci da ya hau kanta, yana mai cewa: “Iran ba ta duba batun Sunna ko Shi’a ba, tana taimakon Falasdinawa ne a matsayin Musulmi da ake zalunta.”
Ya kara da cewa wannan taimako ne ya taimaka wajen samuwar kungiyoyin muƙawama a Iraki, Lebanon, Yemen da sauran wurare.
Hikimar Azumi
A wani bangare na jawabinsa ya yi bayani kan manufar azumi, yana cewa: “Allah ya wajabta azumi domin mutane su samu taƙawa. Don haka bai kamata bayan Ramadan mu koma ga ayyukan sabo ba. Ko da mutum ba zai iya ci gaba da dukkan ibadun Ramadan ba, ya kamata ya ci gaba da yin wasu daga cikinsu.”
Kira Zuwa Ga Yin Addu’a
A karshen jawabinsa, Sheikh Zakzaky ya bukaci musulmi da su kara yawaita addu’o’i domin samun nasarar Jamhuriyar Musulunci ta Iran da kuma kungiyoyin gwagwarmaya, tare da jaddada muhimmancin karanta Suratul Yasin, Fatiha da kuma addu’o’in Sahifa Sajjadiyya.
Your Comment