7 Faburairu 2026 - 21:24
Source: ABNA24
Iran Ta Yi Watsi Da Buƙatar Amurka Ta Dakatar Da Tace Sinadarin Uranium

Iran ta yi watsi da buƙatar Amurka ta dakatar da tace sinadarin uranium gaba ɗaya a ranar farko ta tattaunawa a Oman.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: A cewar wani rahoton sirri Iran ba ta shirya yin watsi da haƙƙinta na tace sinadarin uranium ba. Labarin ya ruwaito cewa Tehran ta yi imanin cewa tawagar Amurka ta nuna "wani sassauci" ga buƙatun Iran amma Iran taki amincewa da shi.

Majiya ta ce batun ƙarfin makami mai linzami na Iran bai taɓa kasancewa a cikin ajandar tattaunawar ba.

Your Comment

You are replying to: .
captcha