9 Yuli 2025 - 22:00
Source: ABNA24
Thomas Barrack: Hizbullah Batu Ne Na Labanon, Amma Babu Wanda Zai Tattauna Da Beirut Har Abada.

Thomas Barrack, wakilin Amurka na musamman a Syria da Lebanon, ya yi nazari kan halin da kungiyar Hizbullah ke ciki da batun ajiye makamanta a wata hira da ya yi da kafar yada labarai ta LBC, inda ya jaddada cewa kamata ya yi a duba wannan batu a matsayin wani lamari na cikin gida na kasar Labanon. Ya kuma yi nuni da irin rawar da Amurka ke takawa wajen gudanar da tattauanwa da kuma rashin sanya wani takamaiman lokaci kan kasar ta Lebanon, ya kuma yi tsokaci kan shirin gwamnatin Lebanon na bayar da hadin kai a wannan fanni.

Kamfanin Dillancin Labaran kasa da kasa na Ahlul Baiti (A.S.) - ABNA – ya kawo rahoton cewa: Thomas Barrack, wakilin Amurka na musamman kan Syria da Lebanon, ya shaidawa kafar yada labaran kasar Lebanon LBC cewa: “Shugaban Amurka Donald Trump yana da jajircewa da mai da hankali sosai, amma abin da ya rasa shi ne hakuri. Hizbullah batu ne na kasar Labanon, ba batun duniya ba. Amurkawa sun sanya ta a siyasance a matsayin kungiyar ‘yan ta’adda, don haka idan suka shiga yaki da mu a ko’ina a matakin soja, kamar yadda shugaban kasa ya bayyana, za su samu matsala da mu.

Barak ya ce "Ajiye makamai na Hezbollah ya kasance mai sauqi qwarai kuma zahirin gaskiya wanda shugaban kasa da sakataren harkokin wajen Amurka ke jaddadawa a kai a kai: kasa daya, al'umma daya, sojoji daya." - Kun ji fa matsiyacin abun da ya ke cewa.-

Ya bayyana cewa, batun ajiye makmai bai shafi makaman Hizbullah kadai ba, har ma da makaman Falasdinawa da mayakan sa kai, kuma idan shugabannin siyasa suka zabi wannan hanya, za mu jagoranci da kuma taimakawa.

Barak ya bayyana cewa ’yan siyasar kasar Lebanon suna buga wasan leda ne, yayin da muke wasan dara. Yanayin da suke nunawa na “ƙarfafawa,” amma suna bukatar su yanke shawarar menene ainihin alkawarinsu. Muna ba su dama su tabbatar da hakan daya bayan daya.

Wakilin na Amurka ya kara da cewa: Kowa yana jin tsoro, babu wanda ke son yakin basasa, babu wanda ke son yin matsin lamba sosai kan kasar Labanon, akwai tsarin addini a kasar ta Labanon da ke bukatar fahimtar juna, dukkanin tattaunawar tana gudana ne a cikin wannan tsarin, muna mutunta tsarin ne kawai.

"Idan ba ku son canji, idan mutane ba sa son canji, kawai ku gaya mana kuma ba za mu tsoma baki ba," in ji shi.

Wakilin na Amurka ya musanta rahotannin jadawalin mika makaman, yana mai cewa, "Ban ce komai ba game da bukatarmu ko martanin Lebanon dangane da jadawalin."

Ya ambaci "kwarewa da jajircewar shugaban Amurka Donald Trump" a matsayin dalilin kasancewarsa a Lebanon.

Dangane da kin amincewar sakatare Janar na Hizbullah Sheikh Naim Qassem na ajiye makamai, Barak ya ce, "Tsarin tattaunawar yana a al'adance a kasar Labanon ne domin aiki ne mai gudana har sai kowa ya shirya tsaf don cimma matsaya ta hakika."

Wakilin Trump ya kara da cewa "Dole ne 'yan Lebanon su tsara jadawalin lokaci kuma mu, a matsayinmu na Amurkawa, muna nan ne kawai don sauƙaƙe amfani da wannan damar cikin sauri amma ba za mu tilasta wani abu ba."

Ya kara da cewa: "Na yi imanin cewa sassan gwamnati a shirye suke, kuma ba shakka ya kamata a gabatar da komai ga majalisar ministocin kasar idan sharuddan da suka dace. Amma sojojin Lebanon su ne babban batu  yanzu."

Game da dangantakar dake tsakanin Lebanon da Syria, Barak ya bayyana fatan cewa "wannan dangantakar za ta bi ta hanyoyi biyu da za su hade nan ba da jimawa ba."

"A halin yanzu, ra'ayin Siriya game da Labanon, Isra'ila, Jordan da Iraki wani bangare ne na wani sabon yanayi, duk inda Syria ta shiga, Lebanon ma za ta bi, saboda Lebanon ita ce kofarsu.

Da yake mayar da martani ga jita-jita game da mamaye birnin Tripoli ko kuma yankunan da ke cikin Darra’a Bekaa zuwa Siriya, Barak ya kuma ce: "Wannan wani zato ne, rudi da kuma wasa, ban ji ko kalma guda ba game da mamayewa ba, kuma babu wani amintaccen mutum a cikin da'irar da ke aiki tare da mu a Siriya da ya yi magana a kai."

A nasa bangaren Barak ya bayyana matakin da sojojin Lebanon suka yi a kudancin kogin Litani tun bayan sanya hannu kan yarjejeniyar a matsayin abin ban mamaki.

Your Comment

You are replying to: .
captcha