8 Disamba 2021 - 13:10
​Syria Ta Ce Hakkin Iran Ne Ta Mallaki Fasahar Nukiliya

Ministan harkokin wajen kasar Syria ya bayyana cewa kamar kowace kasa ta duniya, Iran tana da hakkin ta amfana da fasahar nukiliya domin ayyukan farar hula.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s} - ABNA- Tashar Almayadeen ta bayar da rahoton cewa, a yayin ziyarar da ya kai Iran, ministan harkokin wajen kasar Siriya Faisal Miqdad ya jaddada cewa, yanayin shirin nukiliyar kasar Iran na lumana ne wanda kasar take da hakkin amfana da wannan fasaha bisa dokoki na duniya.

Ya ce abin bakin ciki ne yadda kasashen duniya suke nuna salon siyasar harshen damo dangane da shirin na nukiliya da kuma na wasu kasashe.

Miqdad ya ci gaba da cewa, matukar dai ana son yin adalci kamar yadda manyan kasashe suke ikirari, dole ne a janye dukkanin takunkuman da aka kakaba wa kasar Iran dangane da shirinta na nukiliya, domin kuwa wadannan takunkumai na Amurka sun saba wa ka'ida.

Haka nan kuma ya yi ishara da hakkin Iran na daukar dukkanin matakin da ta ga ya dace dangane da yarjejeniyar nukiliya, sakamakon saba mata alkawali da kasashen yammacin duniya suka yi.

342/