7 Disamba 2021 - 14:52
Aljeriya Ta Baiwa Falasdinu Tallafin Dalar Amurka Miliyan 100

Shugaban kasar Aljeriya Abdelmadjid Tebboune ya sanar da bayar da tallafin dalar Amurka miliyan 100 ga hukumar Falasdinu.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s} - ABNA- "Bisa ga kudurorin da suka dace na kungiyar hadin kan Larabawa, kasar Aljeriya ta yanke shawarar bayar gudunmuwar dala miliyan 100," ga Falasdinu in ji Mista Tebboune a wani taron manema labarai na hadin gwiwa tare da shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas a ziyarar da ya kai birnin Algiers ranar Litini.

Mista Tebboune ya ci gaba da cewa, Aljeriya na fatan sanya batun Falasdinu a ajandar taron kasashen Larabawa da za ta karbi bakunci a watan Maris.

Har ila yau, ya sanar da cewa, kasarsa na shirin karbar bakuncin wani taro nan ba da jimawa ba, da zai hada dukkan bangarorin Palasdinawa, da nufin inganta sulhu tsakanin jam’iyyar Fatah, da kuma Hamas mai rike da iko a Gaza.

Ziyarar da Mr Abbas ya kai kasar Algeriya na zuwa ne kasa da makwanni biyu bayan ziyarar da ministan tsaron Isra'ila Benny Gantz ya kai kasar Maroko, wadda ta harzuka al'ummar Aljeriya da Palasdinawa.

Aljeriya wadda ta yanke huldar diflomasiyya da Maroko a cikin watan Agusta, ta ce ziyarar ministan Isra'ila wata makarkashiya ce kana kuma barazana gare ta.

342/