Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : kasar Iran ya kara da cewa tattsaunawa tsakanin shuwagabannin biyu ya kai na tsawon awa daya da raba, kuma batun daukewa kasar Iran takunkuman tattalin arzikin na zaluncin da aka dora mata shi ne ya mamaye tattaunawar.
A jiya litinin 29 ga watan Nuwamba ce aka koma kan taburin tattaunawa tsakanin kasar Iran da kasashe 4+1 wadanda suka rattabawa yarjejeniyar JCPOA hannu a shekara ta 2015, wadanda kuma suka rage cikin yarjejeniyar bayan ficewar Amurka a shekara ta 2018. Shugaba Ra’isi ya bayyana cewa mataki na farko da za’a dauka a wannan tattaunawar shi ne dagewa Iran wadannan takunkuman kafin aya wata magana.
342/