29 Nuwamba 2026 - 08:41
Source: Al-Mayadeen
Honduras: Akalla Mutane 9 Sun Mutu, Wasu 28 Sun Jikkata A Hatsarin Motar Fasinja A Amurka

Akalla mutane 9 sun mutu, wasu 28 kuma sun jikkata bayan wata motar fasinja ta fada cikin wani kwari bayan ta yi karo da wata karamar babbar mota a kan wata babbar hanya a lardin Comayagua na Honduras.

Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul-Bayt (a.s) – ABNA – ya bayar da rahoton cewa: Mjiyoyin labarai sun ba da rahoton mutuwar akalla mutane 9 da jikkatar wasu 28, a jiya Asabar, bayan wata motar fasinja ta fada cikin wani kwari bayan ta yi karo da wata karamar babbar mota a Honduras, da ke tsakiyar yankin Amurka ta Tsakiya.

A nata bangaren, hukumar kashe gobara ta Honduras ta bayyana cewa wadanda abin ya shafa sun hada da direban motar da wasu maza 3 da mata 5, inda ta yi nuni da cewa har yanzu ba a fayyace dalilan hatsarin ba.

Wani ma'aikacin ceto ya kuma ambata cewa an jefo da wasu fasinjoji daga cikin motar yayin da take fadowa.

Motar, wadda kamfanin "Transportes Carolina" ke gudanarwa, tana kan hanyarta daga babban birnin Tegucigalpa zuwa garin La Esperanza da ke kusan kilomita 170 zuwa yamma, inda hatsarin ya faru a kan wata babbar hanya mai tsananin gangara da lankwasa a lardin Comayagua.

………………

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha