21 Oktoba 2021 - 16:07
Jihadul Islami Ta ce Hadin Kan Musulmi Shi Ne Zai Kare Martabar Palasdinu Da Sauran Kasashen Musulmi

A wata hira da Sakatare Janar din kungiyar jihadul Islami Ziyad Al Nakhalah ya yi da manema labarai a bayan taron makon kadin kai karo na 35 da ake gudanarwa a birnin Tehran yayi tsokaci game da kyautata dangantaka tsakanin wasu kasashen larabawa da HKI inda ya bayyana hakan a matsayin shelanta yaki ne ka Palasdinu da kuma kasashen musulmi.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Har ila yau ya ara da cewa hada kai da HKI tamkar taimaka mata ne ta kalubalancin Alummar musulmi,don haka gudanar da taron hadin kan musulmi mayar da martani ne ga duk wani shirin HKI da kuma kokari kulla hulda da ita ta kowanne bangare

Daga karshe ya ce a yau mun gani cewa hadin kai shi ne aminci da zaman lafiyar Alummar musulmi, da kuma kare Masallacin Qudus daga brazanar Isra’ila

Shi dai taron Makon hadin kan Musulmi an fara shi ne a shekara ta 1990 bisa umarni wanda ya kafa jamhuriyar musulunci ta Iran Imam Khomaini yardarm Allah ta tabbata gareshi, yazuwa yanzu an gudanar da shi har sau 34.

342/