Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Mista Bennett, ya gana da shugaban Masar Abdel Fattah al-Sissi a birnin Charm el-Cheikh, inda suka tattauna kan batun farfado da tattaunawar zaman lafiya tsakanin Isra’ila da Falasdinu.
Dama dai a shekarun baya bayan nan Masar da Isra’ila, sun karfafa alakarsu ta fuskar tsaro musamman yaki da ta’addanci a yankin Sinai, da kuma alaka ta bangaren makamashi, inda tun 2020, Isra’ila ke shigar da iskar gaz dinta zuwa Masar.
Kafin hakan dama Masar na tattaunawa da hukumomin Falasdinu da kuma na kungiyar Hamas dake mulki a zirin Gaza, a wani mataki na neman farfado da tattaunawar zaman lafiya tsakanin Falasdinun da kuma Isra’ila, wacce ta katse tun cikin 2014.
A kwanan baya Isra’ila ta gabatar da wani shiri na farfado da zirin Gaza, amma da sharadin Hamas za ta rungumi zaman lafiya, kan kuma Isra’ilar na bukatar kasra Masar domin cimma manufofinta.
342/