11 Yuli 2021 - 12:24
​Rouhani: Gwamnatin Iran Na Shrin Yi Wa Mutane Dubu 500 Rigakafin Corona A Kowace Rana

Shugaban kasar Iran Hassan Rouhani ya bayyana cewa, gwamnatin kasar na da shirin fara yi wa mutane dubu 500 allurar rigakafin cutar corona a kowace rana a kasar.

ABNA24 : Ya ce kasar ta yi fama da wannan matsala ta cutar corona, kuma an yi kokari matuka wajen shawo kan matsalar yaduwarta cikin sauri, da kuma illar da take yi wa mutane, musamman asarar daruruwan rayuka da aka rika samu a lokutan baya a kowace rana, inda yanzu an samu saukin lamarin.

Shugaba Rauhani ya ce har yanzu akwai sauran sauran barazanar cutar corona a kasar Iran, domin kuwa an iya gano cewa sabon nau’in cutar na Ingila ya shigo cikin Iran ta kan iyakokin yammacin kasar, wato daga kasar Iraki, kamar yadda kuma an gano cewa sabon samfurin cutar daga kasar India ya shigo kasar.

Wannan yasa ala tilas a kara rubanya kokarin da ake yi wajen fuskantar wannan cuta, wanda kuma baya ga hanyoyi na kiyaye ka’idojin kiwon lafiya, dole ne mutane su karbi allurar rigakfin cutar domin samunkariya.

Rauhani ya ce dukkanin mutanen Ira da suka haura shekaru 18, wadanda yawansu ya kai mutane miliyan 60, dole ne su karbi allurar rigakafin cutar, wanda da yardar Allah za a fara yi wa adadin mutane masu yawa wannan allurar nan da ‘yan kwanaki masu zuwa, ta yadda za a kammala aikin cikin kankanin lokaci.

342/