ABNA24 : Shafin yanar gizo na Africa news ya bayyana cewa gwamnatin kasar zata dauki nauyin gasar kwallon kafa ta kasashen Afirka a cikin watan Jeneru mai zuwa, don haka ruka gidajen wadan nan mutane yana daga cikin shitye-shiryen gwamnati na shiri wa wannan wasan.
Wani wanda aka rusa gidansa mai suna Fernand Zepab y ace shekaru 50 ya dade yana tara kudi don gina gida amma yanzu an rusa gida ba tare da an biya shi kudaden diyya ba. Yanzu ina zashi ga yara kanana a gabansa gashi ya tsufa.
Har’ila yau wani mai suna Sulaiman Ben Jaho y ace ina ma da ace sun biya mutanen diyya. Amma basu yi ba.
An ce mafi yawan wadanda suke zaune a kusa da tashar jiragen sama na duala wadanda ambaliyar ruwa ta shekara 1986 ta kora daga yankunansu ne.
342/