13 Satumba 2020 - 11:53
​‘Yan Sanda A Canada Na Bincike Kan Kisan Wani Musulmi A Cikin Masallaci A Toronto

Jami’an ‘yan sanda a kasar Canada sun sanar da cewa, suna gudanar da bincike kan kisan da aka yi wa wani musulmi a cikin masallaci a birnin Toronto.

ABNA24 : Rahotanni daga birnin Toronto na kasar Canada na cewa, jami’an ‘yan sanda na birnin sun ce sun dukufa kan gudanar da bincike, domin gano wadanda suke da hannu a kisan wani musulmi da aka yi a cikin masallacin cibiyar musulmi ta International Muslim Organization of Toronto da ke yankin Rexdale.

Cibiyar ta fitar da bayanin da ke cewa, tana kira ga dukkanin musulmi a birnin da ma kasar ta Canada das u kwantar da hankulansu bayan faruwar wanna lamari, kuma cibiyar tana ci gaba da bin kadun lamarin ta hanyoyin da suka dace.

An kashe mutumin ne a cikin masallaci bayan sallar isha’i, ta hanyar daba masa wuka a bangarori daban-daban a cikin jikinsa, inda a nan take ya rasu a cikin masallacin.

Jami’an ‘yan sada sun ce wasu shedun gani da ido sun tabbatar da cewa sun ga shiga wani mutum ramamme a cikin cikin masallaci sanye da bakaken kaya, daga bisani kuma ya fita daga cikin masallacin, inda bayan haka ne aka fahimci cewa an yi kisan kai a wannan masallaci.

342/