ABNA24 : Darurun manoma a kan motar noma Tractor, Babura, manyan motoci da dawakai sun kwarara a kan manyan hanyoyi a garin Mookgophong na kasar Afirka ta Kudu a ranar Talatar da ta gabata domin nuna rashin amincewarsu kan matakan rashin tsaro da suke fuskanta sakamakon yadda wasu ‘yan daba suke kai musu farmaki a gonakinsu.
Zanga-zangar baya-bayan nan manoman sun gudanar da ita ce da nufin ganin kotu ta zartar da hukunci mai tsanani kan wasu mutane uku da ake zargi da hannu a kashe wani manomi dan shekaru 79 a duniya a watan Maris da ya gabata.
Masu zanga-zangar suna dauke da hotuna masu zanen X a matsayin samfurin neman kawo karshen kashe-kashen gilla kan manoma a duk fadin kasar. Kamar yadda manoman suka bukaci gwamnatin kasar da ta tsaurara matakan tsaro da nufin shawo kan hare-haren wuce gona da iri kan manoma a kasar ta Afirka ta Kudu.
342/