27 Yuli 2020 - 11:23
An Ji Karar Fashewar Wani Abu A Wani Sansanin Sojoji A Birnin Bagadaza

Majiyoyin labarai daga kasar Iraqi sun bayyana cewa an ji karar fashewa har sau biyu a sansanin sojoji na “Assaqar” daga kudancin birnin Bagdada babban birnin kasar.

ABNA24: Kamfanin dillancin labaran Sumariya ya bayyana cewa fashewar ta auku ne a yankin “Abu-Dushir” kan hanyar Bagdaza zuwa Hilla, amma wasu majiyoyi suna cewa zafin rana ya haddasa fashewar.

Amma shafin yanar gizo na Rusiyal-Yaum ya bayyana cewa hare-hare ne aka kaiwa runbun ajiya makamai a sansanin, kuma ana zaton sojojin Amurka ne suka kai harin.

Dakarun Kata’ib Hizbullah da kuma na Badar ne suke zama a sansanin , sannan akwai labarin cewa wasu da dama sun yi shahada sanadiyyar hare-haren.

342/