Yarjejeniyar Nukiliyar Amurka Da Saudiyya

  • Isra'ila Ta Kidime Kan Yarjejeniyar Nukiliyar Amurka Da Saudiyya Wacce Ke Nuna Raguwar Matsayin Isra'ila Ga Amurka

    Isra'ila Ta Kidime Kan Yarjejeniyar Nukiliyar Amurka Da Saudiyya Wacce Ke Nuna Raguwar Matsayin Isra'ila Ga Amurka

    Yarjejeniyar da ke gab da aukuwa tsakanin Amurka da Saudiyya game da haɓaka shirin nukiliya na fararen hula na wannan ƙasa, ta haifar da tashin hankali a cikin muhawarrun Isra'ila. Yarjejeniyar da ke nuna "raguwar matsayin Isra'ila a gwamnatin Amurka," kamar yadda Kafofin yada labaraN Isra’ila suka nakalto daga majiyar gwamnatin, sabanin gwamnatocin baya waɗanda suke danganta duk wata yarjejeniya ta nukiliya da Saudiyya ga ci gaba a hanyar daidaita dangantaka da Isra'ila, wannan sharadi babu shi a yarjejeniyar yanzu.