Madogara : ابنا
Lahadi
4 Faburairu 2024
08:11:32
1435037
Rahoto Cikin Hotuna Na Gagarumin Zanga-Zangar Da Al'ummar Birtaniya Suka Yi Na Nuna Goyon Baya Ga Al'ummar Gaza Da Ake Zalunta

Kamfanin dillancin labaran Ahlul-Baiti (AS) - ABNA ya habarta cewa, dubban al'ummar kasar Birtaniya ne suka fito kan tituna karo na takwas da taken "Dakatar da kisan kiyashi" a birnin Landan, babban birnin kasar, inda suka bayyana goyon bayansu ga yunkurin mutanen Gaza da ake zalunta kuma sun bukaci a tsagaita bude wuta cikin gaggawa.