Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Litinin

16 Janairu 2023

17:47:39
1339021

Ana Ci Gaba Da Neman Sakin Fasfo Na Shekh Zakzaky (H) A Najeriya

Matasa sun sake fita, suna sake Kira ga azzalumar gwamnatin Buhari dasu gaggauta sakin Fasfo din Jagora Sayyid Zakzaky (H) da mai dakinsa Malama Zeenah Ibrahim su tafi neman lafiya, Kamar yadda suka Saba dukkan ranakun litinin da Jumma'a a Abuja suna fita Motsin neman Fasfo din Jagora (H), da Mai dakinsa Malama Zeenah domin su tafi neman lafiya a kasashen ketare. Muzaharar yau litinin 16/1/2023 ta gudana ne tun daga bakin Banex plaza har zuwa Banex Junction dake Wuse 2(!!) Birnin tarayya Abuja.