Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Jummaʼa

11 Faburairu 2022

13:05:18
1228400

Iran Na Bikin Cika Shekaru 43 Da Nasarar Juyin Juya Halin Musulinci

Ana gudanar da bukukuwan cika shekaru 43 da samun nasarar juyin juya halin musulunci a kasar Iran.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA -A shekarun baya dai akan shirya tarurukan gangami a dandalin Azadi da ke tsakiyar birnin Tehran da kuma sauran yankunan kasar domin murnar wannan rana, saidai a shekarun biyu na baya nan an takaita bukukuwan saboda bullar annobar korona.

Kamar dai kowace shekara, 11 ga watan Fabarairu wadda ta yi daidai da ranar 22 ga watan Bahman a kalandar Iraniyawa, al’ummar kasar na murnar zagayowar wannan rana da jagoran gwagwarmaya na kasar Ayatullahi Khomeini ya dawo Iran bayan korar sarki Shah daga karagar mulkin kasar.

Bikin na bana dai na zuwa ne a karkashin shugabancin Ebrahim Ra’isi, wanda ya karbi shugabancin kasar a watan Agustan bara.

342/