Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul-Baiti As - ABNA - ya habarto maku cewa: an gudanar da zaman makokin na daren shahadar Imam Rida As, wanda ya samu halartar al'ummar birnin Qum da kuma maziyarta wadanda suka samu ziyartar hubbaren Karimatu Ahlul-baiti (S) domin yin ta'aziyya, taron ya gudana tare da jawabin Hujjatul-Islam wal-Muslimeen Mandghari, da kuma mai waken jaje Abbas Heydarzadeh a hubbaren Imam Khumaini (RA) da ke haramin Sayyidah Ma’asumah Amincin Allah ya kara tabbata a garesu.

4 Satumba 2024 - 06:25