Yayin da wata mata daga kabilar Bani Bakir da ta ke a cikin rundunar Umar bin Saad ta ga sojojin Kufa sun far wa mata da bukkokin Imam Hussaini (a.s) suna kwashe su da wawashe kayansu, sai ta dauki takobi ta afka wa danginta tana mai cewa: Shin kuna wa 'ya'ya matan Annabi (SAW) fashi? Babu wani hukunci sai hukuncin Allah, ya ku masu neman daukar fansar jinin Manzon Allah (SAW). ▫️Sayyid Ibn Dawus, AlluHuf, shafi na 180 ▫️ Ibn Namayi Hilli, Muthirul-Hazan, shafi na 77
10 Yuli 2024 - 06:57
News ID: 1470938