Digon Hawaye Mafi Nauyi ▪️ Digon hawayen da ake zubarwa a lokacin tuna musibar Imam Hussaini (As) shi ne digon hawaye mafi nauyi a duniya. Imam Riza (a.s) ya yi magana da Ɗan Shabib yana mai cewa: Ya dan Shabib, idan ka yi wa Hussaini (A.S) kuka har hawayenka suka gangaro bisa kumatunka, Allah zai gafarta maka duk wani zunubi da ka aikata, karami ko babba, kadan ko dayawa. ▫️ Amali, Sheikh Sadouq, shafi na 192.

8 Yuli 2024 - 17:03