An gudanar da taron kasa da kasa na Musulunci Addini Ne Ta Tattaunawa Da Rayuwa" a birnin Sao Paulo na kasar Brazil, tare da halartar Ayatullah Reza Ramezani, babban sakataren majalisar duniya ta Ahlul-Bait (AS).wakilin ma'aikatar shari'a ta Brazil, wakilin kungiyar Cardinals na wannan kasa, wasu limamai da mabiya addinin kirista na Sao Paulo, jami'an siyasa na birnin da jihar Sao Paulo da malamai da kuma masu ruwa da tsaki da masu tabligi masu addini na Kudancin Amirka sun halarta.

27 Afirilu 2024 - 11:10