Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya kawo maku rahoton cewa, ofishin yada labarai na gwamnati a Gaza ya sanar da cewa bayan shahadar Jabr Abu Hadros, wakilin tashar tauraron dan adam ta AlQudsul Yaum, sakamakon harin da sojojin haramtacciyar kasar Isra'ila suka kai a sansanin Nusirat, adadin 'yan jaridan da suka shahada tun farkon yakin zirin Gaza a ranar 7 ga Oktoba ya kai 106.

30 Disamba 2023 - 15:46