Kamar Yadda Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - ya kawo rahoton cewa, Magoya bayan Falasdinawa a birnin New York sun gudanar da zanga-zanga a kan titunan birnin Brooklyn na birnin New York na kasar Amurka, a daidai lokacin da ake gudanar da tarukan zagayowar ranar Nukbah shekaru 74 da suka gabata, inda Dubban masu zanga-zangar da suka hada da Falasdinawa, Yahudawa masu adawa da yahudawan sahyoniya da sauran abokan gwagwarmayar Palasdinawa, sun hallara a unguwar Brooklyn don yin Allah wadai da abun da ya faru a irin ranar tare da tunawa da Shirin Abu Aqla, yar jaridar Al Jazeera da ta yi shahada.

22 Mayu 2022 - 18:35