Kamar yadda ingantattun Littafan Shi'a da Sunna suka tabbatar, an haifi Amirul Muminina Ali bn Abi Talib (AS) ne a ranar 13 ga watan Rajab, shekaru talatin bayan shekarar giwa, a birnin Makka a kuma cikin dakin Ka'aba. Wurin da aka tsaga ma mahaifiyar Amirul Muminin (AS) mai daraja ta shiga a yanzu ana kiransa da "Mustajar" kuma yana manne da "Ruknul Yamany". Fiye da shekaru 1440 suka shude tun lokacin. Duk da cewa a cikin wannan dogon lokaci an gyara ginin dakin da Ka'aba da yawan gaske har ma an sake gina shi sau da yawa, amma duk lokacin da aka gyara, gyara da kuma maye gurbin duwatsun sai wurin tsagawa ya sake bayyana.
Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - ya habarta cewa, an haifi Imam Amirul Muminina Ali bn Abi Talib (AS) ne a ranar 13 ga watan Rajab, shekaru talatin bayan shekarar giwa, a birnin Makka da kuma a cikin dakin Ka'aba.
Malaman tarihi na larabawa sun rubuta cewa a lokacin da “Fatima bint Asad” mahaifiyar Imam Ali (AS) ta na nakuda sai ta je dakin Ka’aba ta yi addu’a kamar haka: “Ya Allah! Na yi imani da kai da dukkan annabawa da littattafan da suka zo daga gare ka, kuma ina tabbatar da maganar kakana Ibrahim Khalil wanda ya gina wannan gida Ya Ubangiji! "Da hakkin wanda ya gina dakin nan, da hakkin yaron nan da ke cikina, ka sauwake mini yanayin haihuwarsa.
Bayan wannan addu'ar ne kwatsam sai aka ga dakin Ka'aba ya tsage sannan Fatima ta shiga cikin dakin ta 6uye daga ganin gani da masu sauraro na alhazai, Sannan aka hade bangon dakin kamar da. Mutanen da suka firgita suka so su bude kofar, amma kofar ba ta bude ba, kuma sun san cewa akwai wani sirri a cikin wannan aiki, kuma wannan al’amari na Allah ne.
Wajen da aka tsagawa mahaifiyar Amirul Muminin (AS) a yanzu ana kiransa da “Mustajar” kuma yana manne da “Ruknul Yamani”.
Fiye da shekaru 1440 sun shude tun lokacin. Duk da cewa a cikin wannan dogon lokaci, an sha gyara dakin Ka'aba har ma an sake gina shi; Amma duk lokacin da aka gyara har ma da sauya duwatsun, wurin tsagawar ya na sake bayyana.
Yadda Wurin yake ciki Hotunan Kusa da bangon da ya fashe da aka gyara:
Wani hoto na tazarar da aka maido a wani gyara:
Kwatanta hotuna masu zuwa tare da hotunan da ke sama yana nuna gyare-gyare da yawa a cikin shekaru daban-daban.