Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - ya kawo rahoton cewa, shugaban jamhuriyar musulunci ta Iran Dr. Sayyid Ibrahim Ra'isi ya kai ziyara kabarin shahidan juyin juya halin musulunci a Behesht. Zahra bayan ya halarci taron sabunta alkawari da manufofin marigayi Imam Khumain Rh inda bayan ya Halarta yayi Adduah kan kaburburan da suka hada da: shahidan gidan rediyo da kafafen yada labarai (jirgin sama na c130), shahidan harin ta'addancin da aka kai wa ISIL, shahidan waki'ar Mena, shahidan jirgin Ukraine, shahidan masu kare harami da Fatimidimiyyun, shahidan ma'aikatan lafiya da sauran masu kashe gobara. Shugaban ya kuma ziyarci kabarin shahidan da ba a san ko su waye ba da aka binne a Behesht Zahra inda yayi masu karanta Adduah, inda ya karrama su da tare da tunawa da su hanayar yi masu adduoi.

7 Faburairu 2022 - 14:01