Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - habarta cewa, a safiyar ranar Laraba ne 2 ga watan Fabrairun 2022 ne aka gudanar da jana'izar gawar Ayatullahi Safi Golpayegani, Marji'in abin kwaikwayo na mabiya mazhabar shi'a ta duniya, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti (AS) ya ruwaito a birnin Qum. An gudanar da bikin ne daga karfe 10 na safiyar ranar laraba daga filin Jihad da ke birnin Qum zuwa hubbaren Sayyida Fatemeh Masoumeh (AS) ta hanyar "Titin 19 Dey". Masoya da dama na Maraji'ai da Dalibai addinin a Qum da sauran garuruwan tare da dimbin malamai sun halarci wannan bankwana mai cike da tarihi. Ayatullahi Sobhani Tabrizi, wakilan sauran gidaje na maraji'ai da ake Taqlidi da su na Hojjatoleslam Wal Muslimeen "Muhammady Gulfagani" Da dakaru da dama sun halarci Taro Bayan da jana'izar ta isa haramin Sayyidah Masoumeh (AS), an kai akwatin gawar da ke dauke da gawar zuwa harami, inda aka yi addu'a ga wannan jiki mai tsarki.
Hoto: Hadi Charghani