An gudanar da gasar cin kofin Haj Qassem Soleimani tsakanin kungiyoyin kasar a birnin San'a, kuma kungiyoyin biyu na gasar sun sanya hotonuna Janar Soleimani a jikin rigar su.
Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - ya bada labarin cewa, an gudanar da gasar kwallon kafa ta shahidan Haj Qassem Soleimani a birnin Sanaa tare da halartar kungiyoyin kasa da kasa, tare da taimakon sashen matasa na karamar hukumar babban birnin kasar Yemen.
A wasan karshe na wannan gasa kungiyar Al-Ahly ta lallasa kungiyar ta Al-Shaab da ci daya mai ban haushi kuma ta zama zakaran gasar cin kofin Shahid Qassem Soleimani.
Bayan kammala taron, mataimakin ministan wasanni da matasa na kasar Yemen "Ali Hadban" da kuma darakta da mataimakin daraktan sashen matasa na babban birnin kasar Yemen ya gwangwaje kungiyar Al-Ahly a gasar cin kofin Shahid Qassem Soleimani da lambar zinare da kyautar kudi ita kuma kungiyar Al-Shaab da tazo a matsayi na biyu da lambar azurfa Kuma ya hada da kyautar tsabar kudi.
A cikin wannan biki, mataimakin minista da daraktan ofishin matasa sun yaba da matsayin shahid Soleimani na tallafawa wadanda ake zalunta a duniya.
Tawagogin biyu na wannan gasa sun sanya hoton Janar masoyi ga zukata, shahidi Haj Qasem Soleimani, a jikin rigunansu.
342/