Duk da tsaurara matakan tsaro da sojojin haramtacciyar kasar Isra'ila suka dauka da kuma ruwan sama kamar da bakin kwarya, sama da Palasdinawa masu ibada dubu 30 ne suka gudanar da sallar Juma'a a masallacin Al-Aqsa.
Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - habarta cewa, duk da tsauraran matakan tsaron da sojojin mamaya na haramtacciyar kasar Isra'ila suka dauka da kuma ruwan sama kamar da bakin kwarya, sama da Falasdinawa dubu 30 ne suka gudanar da sallar Juma'a a masallacin Al-Aqsa.
'Yan sandan Isra'ila sun kafa shingayen binciken ababen hawa a mashigar masallacin Al-Aqsa da tsohon yankin Kudus da sanyin safiyar Juma'a, inda suke duba katunan Falasdinawa da tsauraran matakan da suka saba.
Hakazalika sojojin mamaya sun hana wasu 'yan yammacin gabar kogin Jordan shiga masallacin Al-Aqsa do gabatar da da sallah da addu'o'i bisa wasu dalilai.
Dangane da haka, masu fafutuka na Palasdinawa sun yi kira da a kara yawan jama'a da su halarci wajaje masu tsarki domin tinkarar tsauraran matakai na gwamnatin sahyoniyawan.
342/