Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s} - ABNA- ya habarta cewa, an gudanar da bukukuwan cika shekaru shida da kisan gillar da aka yi a garin Zariya a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya wanda ‘yan uwa musulmai na Harkar Musulunci ta Najeriya ta gudanar. Idan dai ba a manta ba a ranar 13 ga watan Disamba, 2015, daidai da 22 ga watan Azar, 1394HS, a lokacin da ‘yan Shi’a ke shirin gudanar da dira tutar murna zagayowar watan haihuwar manzon rahama Muhammad SAWA a Husainiyar da ke birnin Zariya a Najeriya, wanda sojojin kasar da Shirin su da suka riga suka shirya na shafe tare da ruguza musulmi ‘yan Shi'a a Najeriya su ka kai hari zuwa Husainiya Zaria da kuma gidan Hujjatul Islam Wal Muslimeen Sheikh Ibrahim Zakzaki shugaban Harkar Musulunci a Najeriya, inda suka kashe daruruwan 'yan Shi'a da wasu 'yan uwa na Sheikh Zakzaki tare da raunata wasu, inda suka tafi da shugaban Harkar Musulunci ta Najeriya da matarsa.
13 Disamba 2021 - 14:11
Lambar labari: 1208143